Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kungiyar kafafen yada labarai ta yanar gizo mai suna Association Online Media Guild ta taya gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murnar nasarar da ya samu a kotun koli.
A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai ta hannun shugabanta na riko, Abdullateef Abubakar Jos da sakataren kungiyar, Abbas Yushau Yusuf, kungiyar ta bukaci gwamnan da ya yi amfani da nasarar wajen hidimtawa al’umma.
Yanzu-yanzu: Kotun Ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir a matsayin Gwamnan Kano
Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, a ranar Juma’a nan ne Kotun Koli ta mayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano bayan da kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka soke nasarar da ya samu a zabe.
Da dumi-dumi: Kotun Ƙoli ta Yanke Hukuncin Shari’ar Zaɓen Gwamnan jihar Bauchi
Kungiyar ‘yan jaridun ta yanar gizo ce ta tara ‘yan jaridu da suke aikin su a yanar gizo daga sassa daban-daban na kasar nan, dake da hedikwata a Kano.
Kungiyar ta bukaci gwamnan jihar da ya kyautata kyakkyawar alakar da yake da ita da ’yan jaridun yanar gizo, domin Kano ce ta biyu da ta samu dimbin kafafen yada labarai na yanar gizo baya ga jihar Lagos.
Sun bukaci Gwamnan ya kara inganta tsare-tsaren da zasu ciyar da al’ummar jihar kano gaba.