Daga Shehu Husaini Getso
Sabon ma’ajin karamar hukumar Karaye Alh Abdullahi Sunusi Getso ya kama aiki a litinin dinnan.
A lokacin da yake jawabi a sakatariyar karamar hukumar a gaban ma’aikata da daraktan Mulki na karamar hukumar dama wasu daga cikin alummar yankin, Alh Abdullahi Sunusi Getso yace gwamnatin jihar Kano ta bada muhimmanci kwarai da gaske wajen ganin kananan hukumomin jihar Kano na tasarrafi da kudaden al’umma bisa tsarin doka ta dukkannin hanyoyin da suka dace. Yace zai yi duk mai yuwuwa wajen ganin ya baiwa mara da kunya.
Ya bukaci ma’aikatan karamar hukumar dasu bashi cikakken hadinkai da goyan baya don cigaban yankin, sa’annan ya godewa gwamna da mataimakin gwamnan Kano bisa wannan dama da aka bashi don bayar da gudunmuwarsa.
Tunda farko da yake jawabi Daraktan kudi da Mulki na karamar hukumar ta Karaye Alh Aminu Bello Karaye yace zai hada kai da dukkannin ma’aikatan karamar hukumar dama masu ruwa da tsaki a yankin domin cigaban yankin karamar hukumar ta dukkannin fuskokin da suka cancanci hakan.
Da dumi-dumi: Kotun koli ka iya yanke hukuncin shari’ar zaɓen Kano da Legas ranar Juma’a
Alh Bello Karaye yace gwamnatin jihar Kano a yanzu haka ta damu matuka da kokarin ganin ma’aikatan kananan hukumomi na gudanar da ayyukansu yadda ake bukata.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betty Edu
Yayi kira ga daukacin ma’aikatan karamar hukumar da su koma bakin aiki, domin kaucewa fushi na hukuma, ta yadda za’a hada hannu dasu domin cigaban yankin.
Alh Aminu Bello yace zasu zo da tsare- tsare iri iri na kyautatawa ma’aikata da kara musu kwarin gwiwa, ta yadda dai al’ummar karamar hukumar ta Karaye zasu dandani hakikanin romon Mulki na demokradiyya.