AAPU ta Yabawa Ministan Ilimin Nigeria, Bisa Daukar Matakin Bincikar Shaida Digiri Dan Kwatano

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Kungiyar Jami’o’i masu zaman kansu ta Afrika (AAPU) ta yabawa Ministan Ilimi na Najeriya Farfesa Tahir Mamman kan yadda ya dauki matakin binciken badakalar satifiket din wasu jami’o’in.

Ya ce matakin da Ministan Ilimi na Najeriya ya dauka na bincikar lamarin, zai taimaka matuka wajen saukakawa tare da inganta ka’idojin tabbatar da shaidar karatu ta kasa da kasa tare da dawo da kwarin gwiwar dalibai da iyaye.

Kadaura24 ta rawaito Mataimakin sakataren kungiyar, (Yammacin Afirka), Salissou Mamoudou, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Nouakchott na kasar Mauritania ranar Asabar.

Talla

Ya ce kungiyar ta AAPU a matsayin ta ta jami’o’in masu zaman kansu ta Afirka a shirye suke su marawa Ministan ilimi baya a kokarin da yake yi na tantance ayyukan wadannan jami’o’in da ba sa kula da inganci da ka’idojin jami’o’i a nahiyar Afirka.

“AAPU a matsayinta na Kungiya da ke karfafa gwiwar ga jami’o’i su zama wajen bada ingantaccen ilimi da sahihin bincike, za su goyi bayan duk wani matakan da Ministan ya dauka don ceton martabar jami’o’i masu zaman kansu a Afirka,” in ji shi.

Kamfanin Ɗangote ya Bayyana Dalilin Da Ya Kai EFCC Ofishin Su Dake Legos

Yayin da yake kira ga gwamnatin Jamhuriyar Benin da ta dauki matakan da suka dace don duba wannan mummunar dabi’a, mataimakin sakataren kungiyar ya kuma yi kira ga ministan ilimi na Najeriya da kada ya yi amfani da rahoton da ya bankado wacce badakala a matsayin ma’auni na tantance wasu manyan jami’o’i a Afirka.

“Bai kamata rahoton ya zama ma’aunin da za’a yiwa jami’o’in kuɗin goro ba, saboda akwai manyan jami’o’i masu bada ingantaccen ilimi a Jamhuriyar Benin,” in ji shi.

Ya bayyana cewa kungiyar ta AAPU za ta kuma aike da kwamitin binciken zuwa Cotonou da nufin gano hakikanin abin da ya faru bayan haka kuma za ta fitar da cikakken rahoto kan sakamakon kwamitin.

Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano

Ya ce kwamitin da ake sa ran zai gano gaskiyar abin da ya faru, zai mika rahotonsa ga kungiyar nan da kwanaki 10 masu zuwa domin ya yi wa jami’an ma’aikatar ilimi ta tarayya a Najeriya bayani.

Mataimakin sakataren kungiyar ta AAPU ya yabawa jaridar Daily Nigerian ta yanar gizo kan yadda ta bankado badakalar satifiket da ake yi a jami’ar Cotonou inda ya kara da cewa kungiyar za ta gana da dan jaridan a boye domin yi masa godiya.

Ya yi kira ga Tarayyar Afirka da ta amince da jaridar ta hanyar mutunta rahoton ta na binciken kwa’kwaf saboda yin “aiki mai kyau da kishin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...