Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Tun ranar da kotun kolin Nigeria ta saurari shari’ar zaɓen gwamnan jihar kano da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Jam’iyyar NNPP suka daukaka, al’umma suke ta hasashen ranar da za’a yanke hukunci kan shari’ar.

Kadaura24 ta rawaito Gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ne ya shigar da ƙarar domin ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

 

A watan Nuwamba ne Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriya ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC nasara a hukuncin da ta yanke game da zaɓen gwamnan jihar Kano.

Talla

Har yanzu dai babu wani sahihin labari daga kotun kolin dake nuna ranar da kotun zata yanke hukuncin karshen kan shari’ar zaɓen gwamnan jihar kano.

An Bayyana Adadin Daliban da Haramcin Amfani da Digiri Dan Kwatano Zai Shafa a Nigeria

Don haka, ya kamata al’ummar jihar kano su maida hankali wajen kaucewa labaran karya da ake yadawa musamman a shafukan Sada Zumunta, domin kaucewa shiga ruɗani.

Tun bayan hukuncin ake zaman ɗar-ɗar a jihar ta Kano, inda mutane musamman yan yan Jam’iyyar NNPP suka rinƙa fitowa suna zanga-zangar nuna adawa da hukuncin.

Talla

A cikin watan Maris na 2023 ne Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...