Gwamnan Kano Abba Kabir ya sake alkawarin saukewa wasu ma’aikata kabakin arziki

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnatin jihar Kano ta amince za ta rabawa kananan ma’aikata daga matakin albashi na daya zuwa na shida Kayan Abinchi da suka hadar da shinkafa da masa domin rage musu radadin halin da ake ciki.

Gwamnan kano ya bayar da gudummawar buhunan shinkafa, da masara 10,000 ga ma’aikatan gwamnati a mataki na 1 zuwa 6.

Talla

Shugaban ma’aikatan jihar Kano Abdullahi Musa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da sashin wayar da kan jama’a na ofishin shugaban ma’aikata.

 

Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa an yi aniyar bayar da tallafin ne domin tallafawa ma’aikatan da cire tallafin man fetur ya shafa.

Dan Jaridar Da Ya Tona Asirin Digirin Dan Kwatano Ya Koka

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktar wayar da kan jama’a ta Ofishin shugaban ma’aikata na jiha, Binta Nuhu yakasai ta sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

“Bayan kokarin sake duba albashin ma’aikata da za a yi a bana, Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da kokarin inganta jin dadin ma’aikatan jihar.”

Dangote ya faɗo daga matsayin attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka

Shugaban ma’aikatan ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su sake zage damtse wajen inganta aiyukan gwamnati ta hanyar sadaukar da Kai yayin da suke aiki.

Hakazalika a ranar 2 ga watan Janairu, 2024 Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya amince da bayar da kyautar Naira dubu 20, ma’aikata a jihar na tsawon watanni shida a kowane wata na tsawon watanni shida daga 1 ga Disamba, 2023.

Gwamnatin ta kuma amince da bayar da kyautar Naira dubu 15 na watanni uku ga ’yan fansho wanda zai fara daga ranar 1 ga Disamba, 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...