Mujallar Forbes da ke bibiyar harkokin masu arziƙin duniya, ta ce a yanzu hamshaƙin biloniyan nan ɗan ƙasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.
A alƙaluman da Forbes ta fitar na baya-bayan nan, a kan arzikin attajirai a kowacce rana, darajar arzikin Johann Rupert ta kai dala biliyan 10, yayin da Aliko Dangote aka ƙiyasta nasa arzikin a kan dala biliyan 9.7.

Hakan na nufin Johann Rupert mai shekara 73, ya kere attajirin ɗan kasuwa na Najeriya, Aliko Ɗangote a yawan arziki wanda a baya yake riƙe da matsayin.
Dan Jaridar Da Ya Tona Asirin Digirin Dan Kwatano Ya Koka
Aliko Dangote, mai shekara 66, ya koma mataki na biyu a jerin masu arzikin Afirka bayan da dukiyarsa ta yi ƙasa daga dala biliyan 13.5 zuwa dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.
Mujallar ta nuna cewa an samu raguwar kuɗin hamshaƙan ƴan kasuwa kamar Rabiu Abdussamad da darajar arzikinsa ya kai dala biliyan 5.7 da Mike Adenuga wanda nasa arziƙin ya kai dala biliyan 3.1.
Bayanai na cewa raguwar darajar arzikin nasu, ba zai rasa nasaba da yadda darajar naira ke ci gaba da faɗuwa ba, da kuma wasu matsaloli da suka shafi tattalin arziki.
BBC Hausa