Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kungiyar Kwallon Kafa ta Ajiya da Gyaran Hali ta kasa Reshen Jihar Kano wato FC Kano Correctional Tigers ta Lallasa takwararta ta Ma’aikatar Shari’a Reshen Jihar Kano da Ci 6-1.
Kadaura24 ta rawaito tun mintuna 45 na Farko wasan Kungiyar ta Correctional Tigers ta Zura Kwallaye 3 ta hannun dan wasan gabanta Mai suna sadik.

Wanda bayan dawowa daga hutun Rabin Lokaci Kungiyar ta Kara zura Kwallaye 3 ta hannun dan wasanta Mai suna Jameel Tarauni a ragar ta Kungiyar Kwallon Kafa ta Ma’aikatar Shari’a ta Kano.
Wakokin Kannywood 5 Da Suka Fi Shahara A 2023
Wanda a mintuna na 80 na wasan ita ma Kungiyar Kwallon Kafar ta Ma’aikatan Shari’a ta Zurawa Kungiyar ta Ajiya da Gyaran Hali Kwallo 1 a ragar ta FC Correctional Tigers.
A karshe Kaftin din Kungiyar ta Gidan gyaran hali Inspector Abbas Abubakar musa ya yabawa ‘Yan wasansa yadda suka samu gagarumar Nasara a wasan.