Mun kashe sama da Naira Miliyan 160 Wajen gyara makarantar G.G.C Dala – Shugabar kungiyar DOGAA

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Kungiyar tsaffin Daliban makarantar Yan Mata ta G.G.C Dala a Kano (DOGAA) tace ta samar da cigaba masu tarin yawa a makarantar cikin shekaru biyu kacal.

Shugabar Kungiyar tsaffin dalinban ta kasa Hon. Saudatu Sani ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Kano.

“Tun a watan Aprilu na shekarar 2021, yayin taron bikin cikar makarantar shekaru 60 ne, suka iske makarantar cikin wani yanayi na rashin kayan koyo da koyarwa, yanayin lalacewar Ajujuwa, rashin kujerun zama, tebura, karancin ban dakuna, rashin ruwa da kuma rashin kyauwun dakunan baccin dalibai”. Inji Shugabar

Talla

Saudatu Sani ta cigaba da cewa lamarin ya tashi hankalinsu, la’akari da irin yadda sukayi karatu cikin kulawa da kyakkyawan yanayi a makarantar.

“Shiyasa muka fara tunanin yadda zamu bada gudunmawa domin Inganta makarantar, hakan tasa muka fara yin kira ga tsaffin daliban da suka yi makarantar don tattauna yadda za’a shawo kan matsalar, inda muka kafa kwamitoci daga ciki hadda kwamitin yada labarai wanda Hajiya Sa’a Ibrahim da Hajiya Gambo Ahmad suke jagoranta, Saboda abun da mukai yasa Alh. Aminu Alhassan Dantata ya samu labarin kokarin da muke ya kuma bamu tallafin miliyan goma don fara gyaran makarantar, bugu da Kari ya gyara injin Bohol mai aiki da hasken Rana guda biyar”. A cewar Shugabar

Hotunan yadda wata Tirela ta fadi a cikin gadar Hotoro dake Kano

Hon. Saudatu ta bayyana yadda suka yi amfani da wancan tallafi don inganta Ajujuwa da Samar da kujerun zama da sauran kayan koyo da koyarwa, tare da inganta makarantar G.G.C Dala gaba dayanta.

Kididdgar farko da akayi makaranta zata lashe miliyan dari shida da hamsin, hakan tasa wasu daga cikin daliban dake da hali suka shiga bada gudun nawa, da kuma tallafi daga wurin masu hannu da shuni da aka samu ta dalilin Dantata, Wanda adadin kudin yakai miliyan dari da sittin.

Hajiya Saudatu Sani tace sun gina Babban Ofishin (DOGAA) a cikin makarantar da kuma Sakatariyar koyon Sana’oi ga daliban makarantar sai kuma dakin taro Mai daukar Mutane 150.

A fanin tarihi kuwa da suka bincika Shugabar Kungiyar daliban tace GGC Dala makaranta ce mai dunbin tarihi wadda ta zama makarantar yan Mata ta farko a kano, tarihi ya nuna marigayi Sardauna Ahmadu Bello ne ya kirkirota tun bayan ta matan Aure da aka kafa a gidan Makama a nan Kano.

GGC Dala ta yaye dalibai daga sassa daban- daban a Arewacin Najeriya, wanda Dalibar farko ta kasance yar Asalin garin filatu wadda ta fara karatu a ranar biyu ga watan Aprilu 1962.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...