Hayaniya Ta Kaure A Majalisar Kano Kan Kudaden Masarautu

Date:

 

An tayar da jijiyoyin wuya a zauren Majalisar Dokokin Kano, kan kudaden da gwamnatin jihar ta ware wa masarautu a karamin kasafinta na 2023.

Takaddamar ta kaure ne a yayin zaman tantance kwarya-kwaryan kasafin kudi na Naira biliyan 24 da Gwamna Abba Kabir ya gabatar domin amincewar majalisar.

A yayin bibiyan kasafin ne ’yan majalisa suka diga alamar tambaya bayan da suka ga an ware masarautan Kano, Gaya, Rano da Bichi Naira miliyan 2.5 kowannensu, amma aka ware wa Masarautar Karaye Naira miliyan 50 a cikin kasafin.

Talla

A yayin hayaniyar ne shuugaban majalisar, Jibrin Falgore, ya bayyana wa mambobi cewa Masarautar Karaye ce kadai ta kare kasafin da aka ware mata a cikin Masarautar biyar da ke jihar.

Bayan bayanin da shugaban majalisar ya yi musu ne kurar ta lafa.

Rarara ya yi martani ga masu cewa bai kamata ya shiga Siyasar Kano ba

Majalisar Kano ta amince da karamin kasafin N24 na 2023

A karshen zaman dai, Majalisar ta amince da karamin kasafin kudin na karin Naira biliyan 24 a kan kasafin jihar na shekarar 2023.

Amincewar majalisar da kwarya-kwaryan kasafin da Gwamnan ya gabatar mata ya kara yawan kasafin jihar na 2023 zuwa biliyan 350.

A watan da ya gabata ne gwamnan ya gabatar da kwarya-kwaryan kasafin a gaban wa majalisar domin amincewarta.

Shugaban Masu Rinjaye kuma dan majalisa mai wakiltar Dala, Lawan Hussaini (NNPP) ya ce kwarya-kwaryan kasafin kudin zai ba wa gwamnatin jihar damar aiwatar da manyan ayyuka a bangaren ilimi da na kiwon lafiya.

Baya ga haka, gwamnatin za ta samu zarafin biyan kudaden giratuti da fanshon ma’aikatanta da suka yi ritaya.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...