Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar kano ta taya Kungiyar yan jaridu Mata (NAWOJ) murnar cin zaben babbar Sakatariyar Kungiyar ta kasa wadda ta kasance daga Arewa maso yamma kuma ‘yar Asalin jihar kano.
Jawabin taya murnar na zuwa ne ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Kano Hon. Baba Halilu Dantiye lokacin daya karbi bakuncin tawagar Kungiyar a ofishinsa a ranar Talata.
Hayaniya Ta Kaure A Majalisar Kano Kan Kudaden Masarautu
Dantiye yace babu shakka abin taya Murna ne ga babbar Sakatariyar ta kasa kwamarad Wasila Ibrahim Ladan bisa nasarar da ta samu a zaben, kasancewar ta yar Kano kuma Wadda taje takara daga Arewa maso yamma.
“Amadadin Gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf da dukkanin al’ummar jihar muke taya Mata Yan jaridu Murnar samun wannan nasara da kuma yadda aka yi zaben lafiya ba tare da samun wata matsala ba” inji kwamishina.
Kazalika, Kwamishina yaja Hankalin dukkanin wadanda aka zaba musamman Hajiya Wasila daga jihar kano data maida hankali game da duk wani Abu daya shafi Mata, marasa karfi, da kuma yara kasancewar kungiyar ta Mata ce.
Bincikar yanayin da Mata ke ciki da Yara ta hanyar zagayawa zai taimaka wurin samun sabbin dabarun taimaka musu a Gwamnatance musamman matan da suke yankunan karkara”. A cewar Dantiye
Anata Jawabin Babbar Sakatariyar Mata Yan jaridu ta kasa kwamarad Wasila Ladan tace taji dadin shawarwarin da Kwamishina ya bata za kuma tayi amfani dasu har karshen wa’adin mulkinsu don samar da cigaba a kungiyar da kasa baki daya.
A karshe tayi godiya ga Gwamnan jihar kano da kwamishinan yada labarai na jihar da dukkanin wadanda suka bada gudunmawa musamman Shuwagabannin NAWOJ wajen tabbatuwar nasarar data Samu, wacce tace nasara ga jihar kano baki daya ba ita kadai ba.
Kwamarad Hafsa Sani Usman ita ce Shugabar Mata Yan jarida ta jihar Kano, tace ba iya babbar Sakatariya ta kasa Hajiya Wasila Ladan kwamishina yaba shawaraba, har ita da mambobi ya ja hankali kan jajircewa a aiki don cimma gaci, inda yayi Fatan Alkhairi ga Kungiyar NAWOJ da Fatan yanda Allah ya bawa Wasila Ladan Sakatariya ta kasa ya bata Shugabar Mata ta kasa Baki daya anan gaba.