Daga Rahama Umar Kwaru
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da afkuwar gobarar da ta tashi a safiyar Larabar nan, wadda da ta kone ofisoshi 17 a sakatariyar karamar hukumar Gwale.
Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba.
“Mun samu kiran waya da misalin karfe 03:43 na safe daga Abdullahi Hassan cewa gobara ta tashi a sakatariyar Gwale.
Kadaura24 ta rawaito Jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano.
“Bayan samun labarin, mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 03:46 na safe domin shawo kan gobarar,” inji shi.
Hayaniya Ta Kaure A Majalisar Kano Kan Kudaden Masarautu
Abdullahi ya ce benen da aka yi amfani da shi a matsayin ofis mai tsawon kafa 300 x 200 da sauransu, wanda ya kai 17, ya lalace gaba daya.
Ya kuma ce an kona motar motar kirar Peugeot 406, motar Haice guda daya da motar daukar marasa lafiya ta tasha.
Ya ce hukumar na binciken musabbabin tashin gobarar.