Hukumar Kula da Fannin Shari’a ta Ƙasa, NJC ta amince da ƙarin girma zuwa alkalancin kotun koli ga Moore Aseimo A. Adumein, alkalin da ya yanke hukuncin zaɓen gwamnan Kano mai cike da rudani.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na NJC, Soji Oye, ta ce an amince da ƙarin girma ga Adumein, da sauran wasu alkalai da aka daga likafarsu zuwa kotun ƙoli.

Oye ya ce za a rantsar da alkalin da aka yi wa ƙarin girma bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da majalisar Dattawa sun amice.
Dalilin da yasa kotu ta bada umarnin rufe asusun gwamnatin Kano
Ya ce sauran shugabannin kotuna da aka yi wa ƙarin girma, za a rantsar da su ne bayan gwamnonin jihar da majalisar jihar su sun tantance da amincewa da su.
Daily Nigerian