Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar yan jaridu mata ta kasa reshen jihar kano NAWOJ hadin gwaiwa da cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da cigaban Al’umma CITAD, sun shirya taron gangamin wayar da kan Iyaye mata da maza Kan cinzarafi a Unguwar Ja’en a kano.
A Jawabin ta Shugabar Kungiyar Mata Yan jarida ta kano kwamarad Hafsa Sani Usman tace sunyi amfani da wannan lokacin ne da majalisar dinkin Duniya ta ware kwanaki goma sha shida daga ranar 25 ga watan Nuwamba zuwa goma ga watan Disamba don yaki da cin zarafin Al’umma.
Bugu da Kari ta yi kira ga Iyaye Mata dasu Kula da Tarbiyyar ya’yansu, musamman a wannan lokaci domin gudun fadawa tarkon azzalumai.

A nata Jawabin wakiliyar cibiyar fasahar sadarwa da cigaban Al’umma Mai Kula da sashin jinsin Maza da mata Zainab Aminu Ta shawarci Iyayen mu da su daina tsangwamar ya’yansu ta hanyar hantara da nuna musu wariya, domin hakan yana daga cikin nau’in cin zarafi.
Ta Kara da cewa Kofa a bude take ga kungiyoyin guda biyu Wurin tsaya wa tsayin daka ga dukkanin Wanda yake zargin anci zarafinsa, kana ta bukaci a dinga fito da matsala donyin hukunci ga Wanda aka samu da laifin cin zarafi don yazama izna ga al’umma.
Dalilin da yasa kotu ta bada umarnin rufe asusun gwamnatin Kano
Guda daga cikin masu shirya gangamin wayar da Kan Iyaye game da cin zarafin kwamarad Hannatu Sulaiman Abba, tace an zabi Unguwar Ja’en ne a kano sakamakon samun wasu Rahotanni dake da alaka da cin zarafin ya’ya Mata, don haka tayi kira da karfafawa Iyayen gwaiwa wurin bada hadin kai don ganin an checi Rayuwar ‘ya’ya mata.
Daga cikin masu unguwannin da suka halarci taron sunyi tsokaci da dama, in da mai unguwar Madina Malam Abdulshakur Sa’ad ya bukaci Jin irin gudunmawar da Yan jarida Mata da kuma sauran kungiyoyi irinsu CITAD ke badawa Wurin kawo Karshen matsalar.
In da ya samu amsa Daga kowane Bangare cewa samu rahoton da kwarmashi da kuma bibiya na taka muhummiyar rawa Wajen samun Nasara.
A karshe wakilin dagacin Jaen Alh. Sulaiman Sa’ad usman Yayi godiya da zabar yankinsa na Jaen da kungiyoyin biyu sukayi don wayar da Kai, ya kuma yi Fatan jama’arsa za suyi amfani da abinda suka saurara.
Taron dai yasamu halartar masu unguwanni daban-daban, Iyaye Maza da Mata da kuma matasa.