Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umurci shugaban ma’aikatan Abdullahi Musa da ya kula da ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yau a Kano.

Nadin ya biyo bayan hutun jinya da SSG Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya tafi kasar Saudiyya domin neman lafiya.
Dalilin da yasa kotu ta bada umarnin rufe asusun gwamnatin Kano
A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamna Hon. Shehu Wada Sagagi, Shugaban Ma’aikata zai cigaba da kula da ofishin sakataren gwamnatin har sai Dr. Baffa Bichi ya dawo nan da ‘yan makonni masu zuwa.