Daga Aisha Aliyu Umar
Jarumin nan na masana’antar Kannywood Rabi’u Musa wanda aka fi sani da baban Nura ya yabawa Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa sake nada Aminu Dahiru a matsayin babban mataimakinsa na musamman kan harkokin daukar hoto mai motsi da taruka .
” Babu shakka Aminu Dahiru jajirtaccen matashi ne da baya wasa da aikinsa kuma yake da gaskiya da rikon amana da ya cancanci rike kowanne irin mukami”.
Rabi’u Musa Baban Nura ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24.

Yace yana da yaƙinin Aminu Dahiru ba zai taba baiwa shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Kunya ba, saboda kokarin su wajen sauke duk wani nauyi da aka dora masa.
Gwamnatin tarraya ta bayyana dalilan da yasa wasu ma’aikatanta basu sami albashin watan Nuwamba ba
“Ina amfani da wannan dama wajen taya Aminu Dahiru murnar samun wannan Muƙami, tare da fatan Allah ya bashi damar sauke nauyin da Ganduje ya dora masa kamar yadda ya sauke a baya.