Gwamnatin tarraya ta bayyana dalilan da yasa wasu ma’aikatanta basu sami albashin watan Nuwamba ba

Date:

Daga Tijjani Mu’azu Aujara

 

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ma’aikatan wasu hukumomin gwamnatin tarayya ba su samu albashin su na watan Nuwamba ba ne, saboda hukumomin sun karar da kasonsu na kasafin kuɗin wannan Shekarar mai karewa.

Kadaura24 ta rawaito Ministan harkokin kudi, Wale Edu ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labaran fadar shugaban kasa a Abuja.

Wasu hukumomi irin su manyan makarantun tarayya da FRCN, ba su biya ma’aikatansu albashin watan Nuwamba ba.

Talla

“Duk hukumomin da abin ya shafa sun gama kashe kudadensu na kasafin kudi kuma an rufe tsarin da yake Basu damar biyan albashin,” in ji shi

Mista Wale Edu, ya ce gibin na kunshe ne a cikin kasafin da majalisar ta amince da shi kwanan nan.

Yadda Jirgin Sojin Nigeria ya yi ruwan bam a kan masu taron Mauludi a Kaduna

Ya ce ma’aikatarsa ​​”kawai ta sami shawarwari game da gibin a ranar Litinin” kuma ana kokarin ganin an dawo da hukumomin kan tsarin da ya dace domin su sami damar biyan kudaden ma’aikatan na su .

Da yake karin haske kan dalilin da ya sa hukumomin suka karar da kudaden, Mista Wale Edun ya ce wasu hukumomin sun dauki karin ma’aikata ba tare da sanar da ma’aikatar kudi akan lokaci ba.

“Ya kamata hukumomin su gaya mana akan lokaci domin a dauki matakan da suka dace,” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...