Rayukan mutanen da aka kashe a taron Maulidi ya kamata lauyoyi su bi kadi ba dimokuradiyya ba – Isa Bello ja

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Alhaji Isa Bello Ja, guda cikin dattawa a Arewacin Nigeria ya nuna damuwa kan yadda Rundunar sojin Nigeria ta Kai harin bama-bamai aka wasu Mutane da suke gudanar da maulidi a garin Tudun Biri dake karamar hukumar igabi a jihar Kaduna.

“Babu shakka abun da ya faru abun taikaici ne wanda ya kamata a hukunta duk wanda aka samu da hannu a harin ganganci da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dari tare da jikkata wasu da dama”.

Bello Isa Ja ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.

Talla

Yace a kowannan ya sami labarin wasu lauyoyin sun ce sun shirya domin kare yan siyasa da dimokuradiyya, to ya kamata su zo domin tsayawa tsayin daka don ganin an yiwa wadanda aka kashe a kaduna adalci ta hanyar biyansu diyya.

Gwamnatin tarraya ta bayyana dalilan da yasa wasu ma’aikatanta basu sami albashin watan Nuwamba ba

” Ko a shekarun baya haka soji suka kashe wasu fulani da suka taso daga jihar Benue zuwa Nasarawa, amma haka abun yasa ruwa , to wannan ma Muna tsoron kada abun ya tsaya a fatar baki da kuma yin Allah wadai”. Inji Dattijon arziki

Baturiya mai shekara 62 ta yi saukar Alqur’ani a Kano

Yace bai kamata a dai-dai lokacin da aka kashe fararen hula wadanda basu ji ba basu gani ba, wasu lauyoyi su fito yana maganar zasu kare dimokuradiyya ba, inda yace duk dimokuradiyyar da za’a yi ta ba tare da kwanciyar hankali ba bata da wani amfani.

” Ina kira ga Shugaban kasa da Majalisun kasa da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar an hukunta duk Wanda aka samu da sakaci wajen yiwa wadancan mutane kisan kiyashi ba tare da hakki ba”. Inji Bello Ja

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...