Dan majalisar Kiru da Bebeji ya ba da tallafin Naira Miliyan 20 ga wasu kungiyoyin yakin

Date:

 

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Hon. Abdulmumini Jibril Kofa ya sauke kabakin arziki na Naira Miliyan 20, ga wasu shugabanni 513 daga sassa daban-daban a yankinsa .

“Wannan ba shi ba ne karon farko da muka ba da irin wannan tallafi ga wadannan shugabannin na mu, kuma ba zai zama na ƙarshe ba, zamu cigaba da tallafa muku don baku damar sharbar rokon Dimokaradiyya”. Inji shi

Kadaura24 ta rawaito Hon. Abdulmumini Kofa ya bayyana hakan ne lokacin da raba kudin ga shugabannin sassan a ranar lahadi.

Talla

Yace a makwanin biyu da suka gabata ya bayar da tallafi ga kungiyoyin dalibai da sauransu, yanzu Kuma yace wadanda zasu amfana da tallafin na wannan karon sune shugabannin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomin Kiru da Bebeji da na mazabu da kungiyoyin limamai da na mafarauta da dai sauransu.

Yadda Jirgin Sojin Nigeria ya yi ruwan bam a kan masu taron Mauludi a Kaduna

” Ina so ku sani indai batun aiki ne da kuma bada tallafin ragewa al’umma radadin halin da ake ciki ne, to Ina baku tabbacin ku je gida ku yi bacci har da minshari domin yanzu na fara kuma zan yi tayi har sai kunce ya isheku”. Inji Kofa

Dan majalisar ya kuma godewa al’ummar Kananan hukumomin Kiru da Bebeji da bebeji bisa hadin kai da suke bashi har ya fara samun damar cika wasu daga cikin alkawuran da yayi musu yayin yaƙin neman zaɓe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...