Daga Abubakar Mustapha
Rahotanni daga jihar Neja na cewa wasu mutane uku sun bace bayan da wani jirgin fasinja na katako ya kone kurmus, jim kadan bayan tashinsa a unguwar Katcha da ke karamar hukumar Katcha a jihar Neja a ranar Juma’a.
A cewar wani ganau, Abdulmalik Adamu, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yamma jim kadan bayan kwale-kwalen ya kammala lodin kaya da fasinjojin da zasu koma garuruwansu bayan kammala cin kasuwar Katcha wadda take ci mako-mako.

Ya ce matukin kwale-kwalen yana tsaka fa sarrafa injin ne sai kwale-kwalen ya kama da wuta, lamarin da ya tilasta wa fasinjoji yin tururuwar fita daga jirgin domin tsira da rayukansu.
Shirin Dadin-Kowa ya sa samari son yin wuf da ni – Fati Harka
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan Talabijin na Channels, shugaban masu gudanar da sanar kwale-kwalen na Katcha, Dangana Mai kwale-kwale, ya tabbatar da batan mutane uku wadanda yace duk Yara ne , amma bai bayyana musabbabin tashin gobarar ba, sai dai ya ce jirgin ya kone kurmus tare da wasu kayayyaki na miliyoyin naira.
Wasu masunta daga gudanar da harkokin su a wajen sun taimaka wajen kwaso wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su tare da gaggauta nesanta jirgin da ke konewa da wasu .

Jirgin ruwan dai ya ɗauki fasinjoji ne zuwa garuruwan Zakanti, Danbo da wasu yankuna dake gabar ruwan wadanda suke cikin kananan hukumomin Katcha da Agaie a jihar Neja.