Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na taya jagoran tafiyar Kwankwasiyya, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran jam’iyyar na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Alhaji Abba Kabir ya bayyana Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin mutum mai aki’ida, jajircewa, hakuri, juriya da hangen nesa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.

“Akidar ka ta gina dan Adam da kishin talakawa babban abin koyi ne ga dukkan shugabannin wannan zamani” in ji Gwamna Abba.
Yadda Wani Kwale-kwale ya Kama da Wuta Yana tsaka da Tafiya a Ruwa a Jihar Neja
Gwamna Abba Kabir ya kara da cewa manyan nasarorin da Kwankwaso ya samu na nuni da irin yadda yake nuna rashin son kai da kishin kasa wajen yiwa jiharmu da kasa baki daya hidima a koda yaushe.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya kara wa Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso lafiya da basira domin ya jagoranci magoya bayansa zuwa babban mataki cikin kankanin lokaci da yardar Allah.
