Shari’ar Gwamnan Kano: Hukuncin da ya kai Sanata Abbo kasa yar manuniya ce ga yan NNPP – Bashir Rufa’i Lawan

Date:

Daga Aminu Garba Indabawa

 

Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan jihar kano a ɓangaren yada labarai Bashir Rufa’i Lawan ya bayyana hukuncin da kuton daukaka kara ta kasa rashen Abuja tayi game da Shari’ar Sanata Ishaku Abbo dan Jam’iyar Apc a matsayin ‘yar manuniya ga shari’ar dake gaban kotun daukaka karar akan batun kujerar Gwamnan Kano.

Hon Bashir Rufa’I Lawan ya bayyana hakan ne lokacin da yake tautaunawa da jaridar Kadaura24 a kano.

Talla

Bashir yace babu shakka lokaci yayi da ‘ya ‘yan jam’iyyar NNPP da yace an daure da igiyar zato tamau su saduda, a cewar sa tuni jagororin jam’iyyar ta NNPP sun fahimci hakan wanda ya sanya suke ta kokarin ganin sun jiqawa Gwamna mai jiran gado Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa ruwa wajen yawaita nade-nade da bijiro da ayyukan baban giwa duk domin a tunanin su Gwamnatin jam’iyyar Apc da zata zo su shiga cikin matsala.

Yadda aka bude sabon babin sauraren daukaka kara tsakanin Musa Iliyasu Kwankwaso da Yusu Datti 

Bashir ya bayyana cewa dukkan kudadden da gwamatin Abba Gida-gida suke karba daga burgamin gwamnatin tarayya a kirge suke koda a wannan wata gwamnatin ta kano ta karbi zunzurutun kudin da suka kai Naira Biliyan Tara da Miliyan Dari Biyar da Takwas da Dubu Dari Hudu da Hamsin da Naira Dari Shida Da Tamanin Da Bakwai da Kwabo 40 (N 9,508,450,687,40)

“Dan haka nake shawartar Gwamnatin da tayi taka tsantsan domin kifi na kallan mai jar koma. Domin babu shakka zamu binciki kudaden da Gwamnatin ta karba”. A cewar tsohon SSA Information

Tsohon SSA din ya yabawa shugaban jam’iyyar Apc na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake tafiyar da jam’iyyar musamman yana yin yadda ake samar da sulhu da dai-daito a cikin jam’iyyar a guraren da ake da matsala saboda tumbatsar jam’iyyar.

Talla

“Wajibi a jinjinawa Dr. Ganduje saboda kula da yake yi da ‘yan jam’iyyar na Jihar Kano musamman yadda ya bada mukamai daban-daban ciki harda ministoci guda 2 da kuma daukar tsohon kwamishinan yada labarai comrade Muhammad Garba a matsayin shugaban ma’aikatan ofishinsa, babu shakka an ajiye kwarya a gurbintta musamman idan ake yi la’akari da gogewar da comrade din dake da ita”. Inji Hon Bashir Rufa’i Lawan

A karshe Hon. Bashir Ahmad Rufa’I yaja hankalin ‘yan jam’iyyar Apc na jihar kano da su kwantar da hankalinsu su kuma cigaba shirye-shiryen karbar Gwamnati, gami da addu’o’in nasara da kariya domin a cewar sa a daf suke da dawowa kano ya kuma tabbatar da cewar zasu bi kadin kayayyakin da tsohuwar Gwamnati ta siye inda wannan Gwamnati ki ikirarin su suke siya gurin da aka fidda kobo yace dole sa sun yi aman wannan kudi don babu kira babu abinda zai ci gawayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...