Gwamnan Kano Abba Kabir ya kaddamar da shirin tallafin Karo Karatu ga Dalibai 1001

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kaddamar da sake dawo da shirin kai dalibai kasashen ketare don karo karatu , inda a wannan karo dalibai 1001 za su amfana da wannan shiri da za su je makarantu a kasashen duniya don yin karatun digiri na biyu.

A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, yace Rukunin farko na wadannan dalibai su 150 daga cikin 1001 za su bar Najeriya a ranar Juma’an nan don zuwa kasashen da za su je karatunsu.

Wadanda suka amfana karkashin wannan shiri sune masu shedar karatun digiri mai daraja ta daya kuma ‘yan asalin jihar Kano. Tallafin karatun nasu kuma ya kunshi duk abin da ake bukata don guzurin karatu a kasashen Indiya da sauran kasashe da za su je.

Talla

Da yake mika takardun tallafin a wani kasaitaccen biki da aka yi a farfajiyar filin taro da ke gidan gwamnatin Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan aiki dorawa ne kan shirin ba da tallafi da Sanata Rabiu Kwankwaso ya kirkiro a lokacin mulkinsa tsakanin shekarun (2011-2015) kamar yadda yake kunshe cikin kudirin gwamnatinsa kan manyan makarantu na a bunkasa samar da nagartacciyar al’umma.

Yadda aka bude sabon babin sauraren daukaka kara tsakanin Musa Iliyasu Kwankwaso da Yusu Datti 

Gwamnan ya ce baya ga tallafin karatu na ketare, gwamnatin jihar Kano ta kuma mayar da hankali wajen inganta manyan makarantu na cikin gida ta hanyar kara kudade da ake kashe musu da samar da ababen more rayuwa don samun kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa da bincike a makarantun.

Gwamnan ya bukaci wadanda suka amfana da wannan tallafin karatu da su zage damtse wajen ganin sun yi fice a fannoni da suke karatu, ta hanyar mayar da hankali da nuna dattako da mutunta dokoki da rike al’adu da mutuncin al’ummar da suka fito.

Gwamnan Kano ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwa ga daliban Firamare da Sakandire

A nasa tsokaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci wadanda suka amfana da wannan tallafin karatu su zama jajirtattu kamar yadda wadanda suka gabace su suka zama abin koyi.

Talla

Da yake jawabi a madadin sarakunan jihar Kano Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya taya murna ga wadanda suka ci moriyar shirin bayan godewa gwamnatin Kano da ya yi kan wannan namijin aiki, don haka ya kalubalanci daliban su tunkari abin dake gabansu don tabbatar da samun cikakkiyar nasara ta yadda za a yi alfahari da su nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...