Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya amince da nadin mutane 8 a matsayin shugabannin hukumomin dake karkashin ma’aikatan yada labarai da wayar da kan al’umma ta kasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Ga sunayen wadanda aka nada da ma’aikatun da aka tura su :
(1) National Orientation Agency (NOA) — Director-General / CEO — Mr. Lanre Issa-Onilu
(2) Nigerian Television Authority (NTA) — Director-General / CEO — Mr. Salihu Abdulhamid Dembos
(3) Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) — Director-General / CEO — Dr. Muhammed Bulama
(4) National Broadcasting Commission (NBC) — Director-General / CEO — Mr. Charles Ebuebu
(5) Voice of Nigeria (VON) — Director-General / CEO — Mr. Jibrin Baba Ndace
(6) Advertising Regulatory Council of Nigeria (ARCON) — Director-General / CEO — Dr. Lekan Fadolapo

(7) News Agency of Nigeria (NAN) — Managing Director / CEO — Mr. Ali Muhammed Ali
(8) Nigerian Press Council (NPC) — Executive Secretary / CEO — Mr. Dili Ezughah
Shugaban kasar ya bukaci sabbin shugabannin da su gudanar da aiki tukuru don sauke nayin da aka dora musu ta hanyar inganta ma’aikatunsu da walwalar ma’aikatan su.