Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A yau Alhamis ne kotun daukaka kara dake zaman ta a babban birnin tarayya Abuja ta fara sauraron karar da dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam Yusuf Datti Kura na jam’iyyar NNPP ya daukaka , Inda yake ƙalubalantar hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben yan majalisar tarayya ta yi baya.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, kotun sauraren kararrakin zaben yan majalisar tarayya a jihar kano, ta yi hukuncin cewa ta gamsu dan majalisar na kura madobi da garum Malam Yusuf Datti Kura na jam’iyyar NNPP bai ajiye aikinsa ba ya shiga zabe, Inda kotun tace ta tabbatar da Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam.

Rashin gamsuwa da wancan hukunci na Kotun sauraren kararrakin zaben ne yasa Dan majalisar na jam’iyyar NNPP ya garzaya gaban kotun daukaka kara domin ƙalubalantar hukuncin da ta yanke a baya.
Da yake yiwa manema labarai karin haske kan zaman Kotun daukaka karar na wannan rana, guda cikin lauyoyin jam’iyyar APC, wanda kuma shi ne Mai baiwa jam’iyyar APC ta Kano shawara akan harkokin Shari’a Barr. Abdul Fagge, yace kowanne ɓangare na Shari’ar sun yi bayanan da suka kamata su yi a gaban kotun daukaka karar.
Tinubu bai dauko hanyar yin Shekaru 8 a Mulkin Nigeria ba – Sheikh Ahmad Gumi
” Kasancewar basu shigar da bayanan da ya kamata su shigar gaba daya ba, a don haka muka roki kotun data kori karar da suka daukaka, saboda basu shigar da record din gaba dayansa ba, sai daga baya bayan lokacin ya riga ya wuce sannan suka yi kari akan bayanan da suka shigar”. Inji Barr. Abdul Fagge
” Kasancewar sun gamsu basu shigar da bayanan karar gaba daya ba , mun gabatarwa kotun wasu shari’o’i da akai a kotunan gaba wadanda suke nuna cewa in aka kawo suplimentry record (Karin bayanai) da farko sai ka nemi izinin kotu ma cewa zaka kawo tunda lokacin ya wuce, wanda mun gabatarwa da kotu wadannan cases da suke nuna cewa shi kansa daukaka karar ma korarsa ake yi , saboda ya zaman baka shigar da daukaka karar ba ma a yadda ya kamata”. Inji Barr. Fagge
Muhimmiyar Sanarwa Daga Gwamnatin Jihar Kano
Yace bayan kotun ta ji wadancan bayanai, ta kuma saurari gundarin daukaka karar , yace yanzu suna sauraren kotun ta sanya ranar da zata yanke hukunci akan daukaka karar.
A zantawarsa da jaridar kadaura24 lauyan jam’iyyar NNPP Barr. Bashir Tudun Wuzirci yace sun gabatar da bayanansu a gaban kotun ,Kuma sun fahimci cewa alkalan kotun sun gamsu da dukkanin bayanan da suka gabatar musu.

” Magana ce da dama kotun ta rika ta yi hukunce-hunkuce akan shari’u irin wannan, ba yadda zakai ka ce wani dantakara ba dan jam’iyya ba ne kotun da ta yi hukunci bata da hurumin wannan sannan kuma kuskure ne kotun ta yi da ta ce shi wanda muke tsayawan bai ajiye aiki kwana 30 kafin zaben fidda gwani ba”.
“Abun da doka sashin na 66 karamin kashi na daya F cikin baka na kundin tsarin mulkin Nigeria ya nuna cewa mutum zai ajiye aiki ne kwana 30 kafin babban zaben ba, kuma suma basa inkarin wanda muke tsayawa bai ajiye aiki kwana 30 kafin babban zabe ba. Duka Wadannan bayanai mun yi su a gaban kotun kuma kotun ta gamsu”. Inji Barr. Tudun Wuzirci
Dangane da batun shigar da wasu bayanai da suka shafi Shari’ar daga baya, Barr. Tudun Wuzirci yace rashin gano nasa ne yasa APC take waccan magana, Amma kamata yayi su mai da hankali kan gundarin Shari’ar ba wani ɓangare ba.
Ya zuwa yanzu dai dukkanin bangarorin biyu sun ce suna jira ne kotun ta sanar da su ranar da zata yanke hukunci na ƙarshe akan shari’ar da Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam.