Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!
Ana sanar da jama’a cewa In Shaa ALLAH gobe Alhamis za’a rufe gadar sama ta kofar Nassarawa zuwa gidan gwamnati, da kuma ta Obasanjo saboda wasu ayyuka da za a yi a gadojin.

Saboda haka ake sake tunatar da al’ummar jihar Kano musamman masu bin wannan hanya cewa za’a rufe wadannan gadoji, sannan kuma za’a bude hanyar kasa saboda kulle saman na dan wani lokaci da za’a yi.
Minista Wike ya Magantu kan Zargin yiwa addinin musulunci zagon kasa a Abuja
Muna godiya bisa goyon baya da al’ummar jihar Kano ke bamu a ko da yaushe.

ALLAH Ya taimaki jihar Kano da kuma gwamnan Kano Engr Abba K. Yusuf.
Sanarwa:
Engr Marwan Ahmad
Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano.