Gwamnan Kano ya kaddamar da rabon kayan koyo da koyarwa ga daliban Firamare da Sakandire

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa Ilimi shine abu na farko da zata bawa kulawa ta musamman a fadin jihar kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a yayin bikin raba kayan koyo da koyarwa ga makarantu firamare da sakandire dake fadin jihar kano.

Talla

Gwamnan ya ce Samar da wadannan kayayyaki zai taimaka kwarai ga makarantun jihar kano wajen dawo dasu hayyacinsu ya kuma bukace su dasuyi amfani da kayayyakin da aka basu ta hanyar da ya dace

Daga bisani ya bada umarnin da a kafa kwamiti don tantance malaman da suka bada gudummawarsu wajen koyar da dalibai a jihar kano wato yan BESDA yace nan da mako biyu gwamnati zata sasu a sahun maaikatan jihar kano.

Kotun Daukaka Kara ta Bayyana Inda za’a Saurari Shari’ar Zaɓen Kano da Sauran Jihohi

Daya ke nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam gwarzo yaja hankalin dalibai da su dage wajen Neman ilimi ya kuma bukace su dasu zama jakadu nagari a duk inda suke.

A nasa jawabin shugaban majalisa na jihar kano Jibrin Ismail Falgore ya ce majalisa a shirye take wajen bawa gwamnatin jihar kano hadin kai da ba da koyarwa a dukkan makarantu na jihar.

Talla

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...