Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar kano ta ce ya kori kwamishinan ma’aikatar kasa da safayo ta jihar kano Adamu Kibiya da mai baiwa gwamnan Shawara akan harkokin Matasa Amb. Yusuf Imam Wanda aka fi sani da Ogan Boye.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya Alhamis yayin addu’o’in da yan jam’iyyar NNPP suka gudanar a kano, an jiyo kwamishinan da Oga Boye suna kalaman tunzura al’umma kan Shari’ar zaɓen gwamnan Kano da ake dakon hukunci daga alkalan Kotunan sauraren kararrakin zaben gwamnan kano.
Kwamishinan yada labarai na jihar kano Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a daren juma’ar nan.
Ƙarin bayani na nan tafe