Kungiyar kwadago NLC ta sanar da ranar da zata tsunduma yajin aikin gargaɗi

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta sanar da cewa zata tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 2, daga ranar Talata 5 gawatan Satumba zuwa Laraba.

 

Kungiyar tace zata yi haka ne saboda batun cire tallafin man fetur da ya jefa al’ummar kasar nan cikin matsin rayuwa.

Talla

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC Joe Ajaero ne ya sanar da haka a yau juma’a, a wani taron manema labarai da ya gudana a shalkwatar kungiyar dake Abuja.

 

Kungiyar kwadagon ta zargi gwamnatin tarayya da watsi da cigaba da tattaunawa da ita, da kuma rashin cika alkawurran da gwamnatin tarayya tayi musu a yayin ganawar da sukayi a baya-bayan nan.

Dashen bishiyoyi ne kadai zai magance matsalar dumamar yanayi a cikin al’umma – Sarkin Bichi

Wannan mataki ya biyo bayan zanga-zanga da kungiyar kwadagon ta yi a ranar 2 ga watan Agustan da ya gabata, duk dai kan batun tsadar rayuwar da cire tallafin man fetur ya jefa yan kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya tura Shettima a ɓoye ya ziyarci Buhari a asibiti a London – Rahoto

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima,...

Gamayyar wasu kungiyoyi sun bukaci Kotun kolin Nigeria ta gaggauta yanke hukunci kan rikicin Masarautar kano

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gamayyar kungiyar masu fashin baki da...

Gwamnan Kano Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Fadar gwamnati

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince...

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...