Daga Khadija Aliyu
Kungiyar ‘yan kasuwar Kantin kwari ɓangaren yan tebura dake jihar kano ta zabi sabbin shugabannin da za su jagorance ta na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Zaben wanda ya gudana a Kano, ya samu halartar dimbin ‘yan kasuwa, da wakilai daga kungiyoyi daban-daban, da masu ruwa da tsaki na kasuwar.

Wadanda aka zaba sun hada da, Alhaji Ishaq Alkasim Tatari chairman, mataimakin Shugaban I, Alhaji Ali Isah Musa, mataimakin Shugaban II Alhaji Manniru Yunusa Dandago, Sakatare janar Alhaji Musa Umar Sanda, sai Alhaji Akilu Salihu a matsayin mataimakin Sakatare.
Emefiele: DSS ta kama mataimakin gwamnan CBN Kingsley Obiora
Sauran sun hada da, Alhaji Yakubu Baita sakataren kudi, mataimakin sakataren kudi Alhaji Abdulhamid, ma’aji Alhaji Musa Tijjani Thaiba, Mai bincike I da na II, Alhaji Sammmani El- Samad da Alhaji Hassan Muhammad.
Kungiyar kwadago NLC ta sanar da ranar da zata tsunduma yajin aikin gargaɗi
Barista Kabiru Isah Jibril zai kasance mai ba da shawara kan harkokin shari’a, yayin da Alhaji Saifullahi Lawan Ahmed, da Alhaji Usman Sulaiman suka zama PRO I & II.
An zabi jami’in jin walwalar yan kungiyar I & II, da sakatare tsare-tsare , kuma jami’in kasashen waje I & II, sun haɗar da Alhaji Kabiru Ya’u, Alhaji Salisu Adamu Kura, Alhaji Baffa A.Baffa, Alhaji Abubakar Babayo da Alhaji Rabi’u Musa Kabara.
Dattawan kungiyar 6 sun hada da: Alhaji Jamilu Ata, Alhaji Lawan Safiyanu, Alhaji Hassan Muhammad, Malam Mustapha, Alhaji Sulaiman Saleh, Alhaji Abubakar Abdurrahman, yayin da Alhaji Kabiru Sarki Sagagi da Alhaji Auwalu Abdullahi.
Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Ishaq Alkasim Tatari ya yi alkawarin yin aiki kamar yadda kundin tsarin mulki kungiyar ya tanada, domin kare muradun ‘yan kasuwar.