Dashen bishiyoyi ne kadai zai magance matsalar dumamar yanayi a cikin al’umma – Sarkin Bichi

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

Mai martaba Sarkin Bichi Alh Nasir Ado Bayero yayi kira ga al’umma dasu rika dasa Itatuwa domin yaki da Kwararowar hadama da dimamar yanayi kasar baki daya.

 

Sarkin yayi kira a fadar sa lokicin da yake kaddamar da dashe itatuwan wanda Kungiyar Jam’iyyar matan Arewa suka dauki nauyi karkashin Jagoranci Hajiya Ummi Tanko Yasakai suka gudanar.

Talla

” A wannan yanayi da ake fuskantar sauyin yanayi musamman a wannan kasa ta mu, akwai bukatar Al’ummar mu su Maida hankali wajen dashen itatuwa domin magance matsalar da kuma hana kwararowar hamada”. Inji Sarkin

 

Alh Nasir Ado Bayero ya bayyana cewa dashen itatuwan zai magance dimamar yanayi ya kuma godewa Hajiya Ummi Tanko Yasakai bisa zabar Masarautar a cikin wanda zasu amfani da tsari.

Gwamnatin Kano ta Magantu kan Zargin yanka Tashar Mota ta Rijiyar Zaki

” Ya kamata sauran kungiyoyi da gwamnatoci dasu hannu da shuni su taimaka da itatuwan da al’umma zasu dasa don samar da kyakyawan yanayi da zai inganta lafiyar ku baki daya”. A cewar Sarkin Bichi

A jawabinta Shugaban Kungiyar Jam’iyyar matan Arewa Hajiya Ummi Tanko Yasakai, tace zasu gudanar da tsari dashe itatuwan a Makarantun na Kananan hukumomin goma cikin har da Karamar hukumar Bichi, ta kuma godewa Sarkin bisa damar daya basu domin Kaddamar da shirin da kansa.

A wani cigaba Mai martaba Sarkin ya nada Mallam Abbas Isah Usman a matsayi Sabon dagacin Ruwan Tsa dake Karamar hukumar Danbatta wanda ya gaji mahaifinsa sakamakon murabus da yayi sabo da shekaru da Kuma rashin lafiya.

Alh Nasir Ado Bayero ya yi kira da sabon dagaci daya zaman mai tausayi da yin sulhu da talakawansa da tarbatarar da iyaye na tura yara Makaranta da yin musu Allurar rigakafi tare da gargadi sabon dagacin da kada yayi mu’amula da barayin da sanar da hukumomin tsaro da zarar anga wata bakuwar fuska daba a amince da itaba domin dauka mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...