Rage Kuɗin Manya Makarantu: ACF ta Yabawa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) reshen jihar Kano ta ce rage kuɗin manya makarantun gaba da sakandire ga dalibai da gwamnatin jihar ta yi wani juyin juya hali ne abun musali.

 

Da wannan cigaban, duk ’yan asalin Jihar Kano da ke karatu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, Wudil, Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano da Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kumbotso, Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako, Dambatta da sauran manyan makarantu a Kano, zasu rika biyan kaso 50 cikin 100 na kuɗin makaranta a daga shekarar karatu ta 2023/2024.

Gwamnatin Kano ta Magantu kan Zargin yanka Tashar Mota ta Rijiyar Zaki

Da yake tsokaci ga wannan karamcin, shugaban kungiyar ACF, Dokta Goni Farouk Umar ya bayyana matakin a matsayin juyin juya hali da kuma alamar jagoranci na gari da zai bunkasa Ilimi a jihar kano.

Ya nuna farin ciki saboda yadda gwamnatin jihar Kano ta kudiri aniyar maido da shirinta na bayar da tallafin karatu a kasashen waje da aka tsara domin daukar nauyin dalibai 1001, da kuma yadda ta nuna tausayi da ya sa ta biya kudin rajistar Naira miliyan 700 ga daliban jihar Kano 700 a Jami’ar Bayero Kano.

Talla

A sanarwar da Sakataren yada labaran kungiyar Bello S Galadanci, Shugaban na ACF ya lura cewa duka rage kuɗin zai taimakawa iyayen yara wajen biyan kudin makaranta, Inda yace gwamnatin ta yi la’akari da mawuyacin halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a halin yanzu.

Da yake bayyana ilimi a matsayin ginshiki kuma jigo wajen ci gaban al’umma, Goni Farouk ya yi addu’ar samun nasarar aiwatar da manufofin gwamnati na tallafawa marasa galihu. Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin al’umma da su tallafa wa ci gaban ilimi ta kowace fuska.

A farkon makon nan ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da rage kudaden rijistar da kaso 50 cikin 100 domin inganta Ilimi da kuma saukakawa al’umma sakamakon mawuyacin halin tattalin arzikin da al’umma ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...