Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayar da umurnin fitar da jakadan Faransa da ke ƙasar, inda ta ce a yanzu ya rasa kariyarsa ta diflomasiyya.
Mista Sylvain Itte ya ci gaba da zama a Nijar duk da cikar wa’adin sa’o’i 48 da aka ba shi na ya fice daga cikin ƙasar a ranar Juma’ar da ta gabata.

BBC Hausa ta rawaito Sai dai gwamnatin Faransa ta bayyana cewa jakadanta a Nijar bai zai fice daga ƙasar ba saboda gwamnatin sojojin ba ta da hallaci.