Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kwamitin kar ta kwana kan harkokin man fetur a jihar Jigawa ta rufe wani gidan mai mai suna IMG da ke Dutse bisa laifin tauye litarsu ga masu mu’amala da su.
Shugaban kwamitin, Kanar Muhd Alhassan (rtd) ya ce sun rufe gidan man ne bayan wata ziyarar bazata da suka kai gidan man da ke babban birnin jihar.

Alhassan ya ce duk da gargadin da aka yi wa gidajen mai, IMG Petroleum su ki gyara mitarsu kuma bai mallaki ma’aunin man ba wanda ake kira da paraffin.
Nijar ta umarci ‘yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga ƙasar
A cewarsa, a kowace lita 10, gidan mai na rage wa abokan cinikin litar lita 1.4, kwatankwacin kusan N900.
Ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar ba za ta nade hannunta ta rika kallon wasu tsirarun mutane su rika aikata munanan dabi’u don cutar al’umma .
Gwamnatin Kano ta Magantu kan Zargin yanka Tashar Mota ta Rijiyar Zaki
DAILY POST ta rahoto cewa rundunar ta yi alkawarin fallasa sunayen gidajen man da aka gano suna tauye litar mai ga abokan mu’amalar su ba.
Shugaban ya bayyana cewa kwamitin zai ci gaba da kai ziyarar gani da ido zuwa gidajen mai da ke fadin jihar.