Auren Zawarawa: Mun Sayo kayan Dakin Ma’aurata 1,800 – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki da sauran kiyayyakin ma’aurata 1,800 a karkashin shirinta na aurar da zawarawa .

 

Babban kwamandan hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana haka a lokacin da ya duba wasu kayayyakin auren a ranar Laraba a Kano.

Talla

Ya ce gwamnati ta ware sama da Naira miliyan 800 don siyan kayan sawa, kayan abinci, kayan daki, da sauran kayayyakin bukatu na bikin aure.

 

“Kowace Amarya za ta samu katifa, matashin kai, da kuma Naira 20,000 domin fara sana’a.

Yanzu-Yanzu: NNPP ta dakatar da Kwankwaso

“Wasu masu hannu da shuni sun yi alkawarin bayar da gudummawar kason su don ganin an samu nasarar gudanar da auren zawarawar.

“Ma’aurata 1,800 za su amfana da wannan shirin, wanda zai taimaka matuka wajen dakile munanan dabi’u da talauci a tsakanin al’umma, saboda akan dage aure da yawa, saboda rashin abun da iyaye zasu aurar da ‘ya’yansu ,” inji shi.

Daurawa ya ce za a sanar da ranar daurin auren ne domin baiwa mazauna yankin da masu sha’awar bayar da gudumawar kason su domin cimma nasarar da ake da bukata.

Ya kara da cewa an gindaya sharudda na zabar wadanda za su ci gajiyar shirin, ya kara da cewa wadanda suka saki matansu ba da wani dalili mai kwari ba, sai sun biya gwamnati kudin da ta kashe musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...