Yanzu-Yanzu: NNPP ta dakatar da Kwankwaso

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari sun sanar da dakatar da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon watanni shida saboda zarginsa da yiwa jam’iyyar zagon kasa a zaben daya gabata.

 

Kwamitin amintattun sun fitar da sanarwar dakatarwar ta Kwankwaso a ranar Talata, 29 ga watan Agusta kamar yadda aka wallafa a shafin TVC News.

Talla

Kwamitin amintattun dai ya ce ya ɗauki wannan matakin kan Kwankwaso ne saboda zarginsa da cin amanar jam’iyyar ta hanyar yiwa jam’iyyar APC aiki a zaben shekara ta 2023.

Gwamnatin Kano ta musanta kin tantance wasu daga cikin ma’aikatan da Ganduje ya ɗauka

Rikici dai ya barke a jam’iyyar bayan dakatarwar da aka yiwa dan takararta na shugaban kasa kuma jagoran ta na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakan ya biyo bayan dakatarwar da sakataren yada labaranta na kasa da wasu suka yi a baya, matakin da kwamitin amintattu ya yi watsi da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...

Hukumar almajirai da yaran da ba sa zuwa Makaranta ta kaddamar da yi wa yaran da ba sa zuwa Makaranta Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...