Rashin biyan albashi: Likitoci a Zamfara zasu tafi yajin aiki

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin mako guda ta biya ma’aikatan lafiya 17 albashinsu na wata hudu da sauran ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Yarima Bakura ko kuma su shiga yajin aiki.

 

Shugaban Kungiyar na jihar, Dakta Sanusi Bello, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar, ya kuma bayar da misali da albashin dukkan likitocin asibitin na watan Yuli 2023, da alawus na wata takwas ga kwararrun likitoci da ba a biya, wanda ya sa suka daina aiki.

Talla

Bello ya ce kungiyar ta yanke shawarar bayar da wa’adin mako guda ga gwamnatin jihar Zamfara domin ta magance wadannan bukatun.

Tinubu yana jagorantar taron majalisar zartarwarsa na farko

Ya kara da cewa ƙungiyar a Zamfara za ta ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 4 ga Satumba, 2023, idan har gwamnati ta kasa biya musu bukatunsu.

Shugaban ya yi gargadin cewa matakin zai kai ga rufe dukkanin asibitocin da suka hada da asibitocin gwamnatin tarayya da asibitocin jiha da asibitoci masu zaman kansu da kuma janye duk wani aikin lafiya da na hakori da duk likitocin jihar Zamfara ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...