Shari’ar zaɓen gwamna: Kwankwaso, Gwamnan Kano, da Wasu Sunyi Addu’a ta Musamman Domin Neman Nasara

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin jihar Kano ta shirya addu’o’i na musamman tana mai roko ga Allah da ya tarwatsa shirin masu kokarin kwace musu gwamnati ta bayan fage .

 

Sallar wadda aka gudanar a Filin Mahaha da ke kan titin BUK a ranar Asabar ta samu halartar jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam tare da sauran manyan jiga-jigan gwamnatin jihar.

 

Dr. Sani Ashir ne ya jagoranci sallar.

Talla

A cikin jawabin da ya gabatar Dr. Sani Ashir ya bayyana cewa “Ya Allah, ga shugabanninmu, wadanda muka zabe da karfin ikonka ka kare mana su daga sharrin Masu sharri .

Cikakken bayanin yadda Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Abba Kabir Yusuf

“Ya Allah makiyan al’umma suna ta makirci da shirin bata shugabanninmu, Ya Allah! Ka rusa shirinsu.

“Ya Allah ka kawo mana zaman lafiya mai dorewa a jiharmu. Ya Allah ka albarkaci kasuwanninmu da makarantunmu. Ya Allah ka albarkaci kasuwancinmu da gonakinmu. Ya Allah ka albarkaci shuwagabannin mu, ka halakar da makiyansu.”

Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar

Kadaura24 ta ruwaito cewa jam’iyyar APC na kalubalantar nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf a kotun sauraron kararrakin zabe.

Kotun a ranar Litinin bayan da bangarorin Shari’ar suka mika rubutaccen bayaninsu na karshe ta dage ranar yanke hukuncin zuwa ranar da zata sanar nan gaba.

Kafin wannan lokacin dai ana zargin wasu lauyoyin da laifin bada cin hanci ko yunkurin baiwa mambobin kotun sauraren kararrakin zabe cin hanci a madadin wadanda suke karewa, wanda hakan ya janyo zarge-zarge tsakanin APC da NNPP a jihar.

A makon da ya gabata wasu yan jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin kungiyoyin farar hula ta Kano, sun yi zanga-zanga, Inda sukai tattaki zuwa gidan gwamnati kuma suka mika kokensu ga gwamnan jihar domin ya mika koken nasu ga shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...