Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa nan mai suna Aisha Humairah ta baiwa masoyanta wadanda suke son zuwa wajenta koma wajen wasu jaruman shawarar su daina zuwa kai tsaye don gudun samun matsala.
” Mutane da yawa sun taso daga wasu garuruwan domin ganin jarimai ba tare da sun San koda wanda zai haɗa shi da jarumin ba, kuma hakan yana jefa su cikin mawuyacin hali”.

Aisha Humairah ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi bakuncin Wani yaro Mai suna Adamu da ya zo ganinta tun daga jihar Bauchi .
Shugaban Mulkin Soji na Nijar ya bayyana lokacin da zasu mika Mulki ga farar hula
” Mutane da yawa da suka sanni sun tura min da hoton wannan yaron da yazo wajena , kuma lokacin ma ni bana gari, amma Ina dawo jiya (Juma’a) na neme shi kuma ga shi mun hadu da shi”. Inji Aisha Humairah
Aisha Humairah ta nuna farin cikinta saboda yadda yaron ya taho ta kanas ta kano saboda ita har zuwa Kano, Amma ta bukace shi da kada ya sake ya sake yin hakan saboda hatsarin da zai iya shiga.
Yaron dai mai suna Adamu ya zo Kano ne daga jihar Bauchi saboda ya ga Aisha Humairah Saboda yadda take burge shi a fina-finai da wakokin da take hawa a shafukan sada zumunta.