Daga Aisha Sani Bala
Gwammantin jihar Kano tace zata ci gaba da wasu ayyukan tituna masu kilo mita 5 da aikin su ya tsaya a wasu kananan hukumomin a fadin jihar.
Kwamishinan ma’aikatar Ayyuka da gidaje ta jihar Injiniya Marwan Ahmad ne ya bayyana hakan, yayin da ya jagoranci ziyarta wasu daga cikin kananan hukumomi da aka ci gaba da ayyukan.

Injiniya Marwan Ahmad ya kuma ce ma’aikatar sa a shirye ya take tsaf domin ganin ta kammala aikin titinan a cikin kankanin lokaci.
Shugaban Mulkin Soji na Nijar ya bayyana lokacin da zasu mika Mulki ga farar hula
” Zamu tura ma’aikata dukkanin kananan hukumomin da ba’a karasa aikin titinansu masu tsahon kilomita 5 ba, domin yin aiki tukuru don kammalawa cikin lokaci kamar yadda gwamna ya bamu umarni”. Inji Kwamishinan
Wasu daga cikin al’umma yankin Gezawa da Albasu da kwamishinan ya ziyarta sun bayyanawa koken su kan matsalolin da lalacewar titunan ke haifar mu su musamman a wannn lokacin na damuna.
A baya dai Gwamnan jihar Kano injinya Abba Kabir Yusuf ya zabi wasu kananan hukumomi guda biyar domin ci gaba da ayyukan titunan masu kilo mita 5
Wakiliyar mu Aisha Sani Bala ta rawaito cewa Injiniya Marwan Ahmad ya ziyarci aikin kananan hukumomin Gezawa da Albasu ya Kuma ji koken mazauna yankin tare da yi musu alkwarin kammala aiyukan Titunan da wuri domin gujewa ambaliyar ruwan da ke haifar musu.