Muna goyon bayan ECOWAS ta dawo da Mulkin Dimokaradiyya Nijar – yan Nijar mazauna Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Al’ummar Jamhoriyyar Nijar wadanda suke zaune a jihar kano dake arewacin Nigeria sun nuna goyon bayansu ga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS ta mayar da Muhammad Bazoum a matsayin Shugaban ƙasar Nijar don cigaba da inganta rayuwar al’ummar ƙasar.

 

“Muna nunawa duniya rashin jin dadinmu da yin Allah wadai da yadda sojoji a ƙasar mu ta Nijar suka hambarar da gwamnatin dimokuradiyya wacce Shugaban Muhammad Bazoum ke jagoranta, babu Shakka mu al’ummar Nijar muna son Bazoum saboda yadda ya ɗauki hanyar gyara mana kasa “.

Talla

Shugaban kungiyar yan Kasar Nijar mazauna jihar kano Alhaji Lauwali Mamman Barma ne ya bayyana hakan yayin wata zanga-zangar lumana da suka gudanar a Kano.

 

“Muna goyon bayan kokarin da Kungiyar ECOWAS da sauran kasashe suke yi na dawo mana da zaɓaɓɓen Shugaban kasa Muhammad Bazoum kan Mulki Ƙasar mu ta Nijar, amma muna fatan zasu kwato mukin ba tare da anyi yaƙi ko wani ya rasa ransa ba, Amma babu shakka muna goyon bayan su”. Inji Lauwali Mamman Barma

ECOWAS ta Sanya Ranar da Zata Fara Yakar Jamhoriyyar Nijar

Shugaban yan Nijar mazauna jihar kanon ya yaba da irin matakan da kungiyar ECOWAS take dauka tun lokacin da akai juyin Mulki na ganin an mayar da Muhammad Bazoum kan karagar mulkinsa.

 

” Wannan juyin Mulki an yi shi ne ba bisa ƙa’ida ba, kuma basu da hujjar yinsa, don haka muna so a bamu mulkinmu ba tare da wata hayani ba ko a zubar da jini Wani a kasar mu ba.

Jarumi Aki ya bayyana dalilin da ya sa yake boye matarsa da ya’yansa ga shafukan sada zumunta

Daga ƙarshe Lauwali Mamman Barma yace suna fatan kungiyar ECOWAS zata mayar da Muhammad Bazoum kan karagar mulkinsa ba tare an sami wata matsala ba .

Idan dai za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a watan da ya gabata ne sojojin Kasar Nijar suka hambarar da gwamnatin Muhammad Bazoum ta hanyar juyin Mulki, Inda suka Sanya Abdulrahmani Taichini a matsayin Sabon Shugaban Kasar.

Hakan tasa kungiyar ECOWAS ta fata kokarin ganin ta mayar da Muhammad Bazoum kan karagar mulkinsa, Amma dai tun a wancan lokaci sojojin ba su saduda ba, duk da irin barazana da takunkuman da kungiyar ta rika kakabawa Kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...