Al’umma suna cin wani hali ya kamata gwamnatoci su fito da hanyoyin saukaka musu – Sarkin Bichi

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

 

Mai martaba Sarki Bichi Alh. Nasir Ado Bayero yayi kira da masu ruwa da tsaki dasu bi hanya difilomasiya wajan warware rakici kasar Niger.

 

” Akwai hanyoyi mafi sauki na diflomasiyya da ya kamata abi don warware matsalar, ba lallai sai an yi amfani da karfin soji ba, wanda hakan zai jawo a rasa rayuka da yawa”. A cewa Sarkin Bichi

Talla

Sarkin yayi kiranne yayi daya jagoranci zikiri shekara-shekara tare da addu’ar samun zaman lafiya a kasar wanda ya gudana a Masarautar ta Bichi.

 

Alh Nasiru Ado Bayero ya kira Gwamnati tarraya Gwanatocin Jahohin dasu fito da hanyoyin saukakawa jama’a mai dorewa sakamakon tsadar kayan abinci da sauran kayan masarufi, wanda cire tallafi man fetir ya haifar.

Muna goyon bayan ECOWAS ta dawo da Mulkin Dimokaradiyya Nijar – yan Nijar mazauna Kano

” Al’ummar mu suna cikin mawuyacin hali don haka Muna kira da gwamnatoci a dukkanin matakai da su fito da tsare-tsaren da zasu saukakawa al’umma halin da ake ciki”. Inji Alh. Nasiru Ado Bayero

 

Sarkin na Bichi yayi adduar samun zaman lafiya da walwala arziki a Kasa baki daya.

Bai kamata Hisbah ta bar G-Fresh Al-ameen da Sadiya Haruna haka ba –  Faruk Malami Sharada

A jawabinsa na maraba yayi taro zikiri Babba limamin masarautar Sheik Khalifa Lawan Abubakar ya fadi falaloli zikiri tare da kira da jama’a musulmi dasuyi koyi da halaye Annabi Muhammad saw domin samun tsira duniya da lashira.

A nashi jawabi Shugaban Kwamiti Shirya taro zikiri na shekara shekara Dr Nazifi Ishak Bichi yace amfara taro zikiri shekara-shekarane a karamar hukumar Bichi tun kimani shekaru Goma Sha bakwai da suka gabata bayan amince Marigayi Sarki Kano Alh Dr Ado Bayero.

Taro zikiri ya samun halarta Manya Malamai da dama daga sasan jahar Kano da Kuma Manaja daratar hukumar Samar da ruwan sha ta Jahar Kano Injiniya Garba Ahmad Bichi, Mai bawa Gwamna Shawara akan harka tsartar mahaili Injiniya Abdullahi Shehu Bichi da Kuma Shugaban Jami’ar Gwamnatin tarraya da Dutsima Ferfesa Arma yau Hamisu Bichi da Kuma dukkan hakiman Masarautar ta Bichi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...