Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A ranar Asabar ne tsohon shugaban mulkin soji a Nigeria, Janar Abdulsalami Abubakar (rtd), ya gana da hambararren shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum.
Abdulsalami ya jagoranci wata tawaga mai karfi ta kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS zuwa kasar da ke fama da rikici a yammacin Afirka.

A yau Asabar ne suka isa kasar a wani yunkuri na diflomasiyya na karshe don ganin an cimma sulhu da gwamnatin mulkin Nijar cikin lumana.
Sojojin Nijar sun fara daukar yan sa kai don kare kasar daga harin ECOWAS
Tawagar ta gana da firaminista Ali Lamine Zeine wanda ya tarbe su a filin sauka da tashin jiragen sama ya kuma kai su fadar shugaban kasa.
Sun gana da Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban gwamnatin mulkin soji, da tawagarsa na kusan mintuna 90 sannan kuma shugaba Mohamed Bazoum.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Abdulsalami ya ce, “Mun hadu da shi kuma muka ji ta bakinsa. Ya gaya mana abin da aka yi masa da kuma kalubalen da yake fuskanta. Za mu sanar da wannan ga shugabannin ECOWAS. Yanzu haka dai kofofin tattaunawar a bude suke domin samun maslaha mai dorewa.”
Tsohon Shugaban Kasar bai yi cikakken bayani kan tattaunawar da aka yi da hambararren Shugaban kasar ba.