Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya, ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin hukumar da ke kula da sufurin jirgin kasa ta Najeriya cewa ƴan bindiga na kitsa kai hari daga kowane lokaci a layin dogo da ya hada Kaduna zuwa Abuja.
Babban daraktan hukumar ta DSS reshen birnin Abuja, R.N. Adepemu, cikin wata wasiƙa ya ce an yi wannan gargaɗin ne domin ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakan tsaro a kan wannan hanya, kana ta bayar da shawarwarin da suka dace a ɗauka.

Wasikar ta ci gaba da cewa, bayanan sirri da aka samu sun tabbatar da wannan shirin na kai mummunan harin daga kowane lokaci a yanzu.
Ya ce maharan na shirin amfani da irin salon da suka taɓa bi a baya wajen kai harin, inda suke shirin kai hari tare da sace fasinjoji domin neman kudin fansa.
Wata kungiya mai zaman kanta a Arewa, ta karrama hadimin Ganduje, Aminu Dahiru Ahmad
Daga cikin matakan da hukumar ta nemi a ɗauka sun haɗa da amfani da jiragen sama domin shawagi a wuraren domin lura da abubuwan da ka je su zo, wanda ya haɗa da gudanar da sintirin a kan hanyar da kewayenta.
Haka kuma hukumura ta DSS ta nemi a samar da ƙarin jami‘an soji da yan sanda don gudanar da binciken jama‘a da ababen hawa da baza jami’an tsaro a dazukan Byazhin da Jibi da dazukan Ja, haɗi da samar da na’urorin sadarwa ga jami’an sintiri na ƴan sanda da kuma samar da wata tawagar ƴan sandan ko-ta-kwana waɗanda aikinsu shi ne kai ɗaukin gaggawa a lokocin buƙatar hakan, tare da samar da tsarin tattauna bayanan sirri da suka shafi tsaro a tsakaninsu.
Shari’ar zaɓe: Gwamnatin Kano ta Magantu kan Cin hancin da aka yi yunkurin baiwa alƙaliya
Wasikar ta ci gaba da cewa, duk da ya ke wannan bayanin da aka yi hasashen aukuwar sa, bai fito sarari ba, amma zai iya jefa fargaba sakamakon neman samar da tsaron dukiya da rayukan jama’a da ke zirga-zirga akan wannan hanyar, inda hukumar ta nemi kada a ruruta labarin har ya zarce yadda aka bayyana shi.
Kazalika hukumar ta DSS ta ce yin wanan gargaɗi a kan lokaci na da manufar kaucewa maimaita abinda ya taba faruwa da farko ne, inda aka samu mummunan harin da ya kai ga wasu fasinjoji sun rasa rayuwarsu kana wasu su ka jikkata, baya ga yin garkuwa da wasu, da ƴan bindigar suka yi na tsawon watanni kafin su kai ga samun ƴanci, bayan biyan kuɗin fansa.