Ƴan majalisa a Ghana sun gargaɗi shugaban ƙasar kan tura sojoji Nijar

Date:

Ƴan majalisa ɓangaren marasa rinjaye a Ghana sun nuna adawa kan matakin da Ecowas a ɗauka na shirin afka wa Nijar a matsayin wani yunkuri na dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.
Nijar.

“Majalisar dokokin Ghana ba ta tattauna ba kan lamarin kamar yadda sauran ƙasashe suka yi har ma da ɗaukan mataki, in ji Samuel Ablakwa, wani ɗan majalisa a kwamitin kula da harkokin ƙasashen waje.

Talla

Ƴan majalisar sun gargaɗi Shugaban ƙasar, Nana Akufo-Addo cewa ya dakatar da shirin tura sojojin ƙasar domin zuwa

Ya ce Shugaba Akufo-Addo ba sai ya ji ta baki ƴan ƙasar Ghana ba kan lamarin , saboda tura sojoji Nijar ba shi ne mafita ba.

Dalilai Guda 10 da DSS ta bayar kin Amincewa da El-Rufai a matsayin Ministan Tinubu

BBC ta rawaito yan majalisar ƙasar ɓangaren marasa rinjaye sun ce abin da ya kamata a yi shi ne bin hanyar diflomasiyya da kuma tattauna.

“Ba abu mai kyau bane tura sojojin Ghana zuwa Nijar domin zub da jini, kuma muddin ba a yi hankali, abin zai sake jefa yankin cikin tashin hankali,” in ji Mista Ablakwa.

Ƴan majalisar sun ce ya kamata a yi amfani da kuɗin da ake da shi wajen warware matsin tattalin arziki da ƙasar ke fusknta baya nciyo rancen $3b daga Asusun IMF maimakon tura sojoji zuwa faɗa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...