Zikirin Shekara: Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya ta bayyana matsayata kan juyin mulkin Nijar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Majalisar Koli ta Darikar Tijjaniyya ta yi kira ga al’ummar Musulmin Nigeria da su maida hankali wajan yin Addu’oi domin warwarewar matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassa Kasar nan da kuma tsadar rayuwa da ake ciki yanzu.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da Shugaban kwamitin yada labarai Malam Ibrahim Inyas Abubakar da Sakataren yada labaran kwamitin majalisar Shuran Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Talla

Sanarwar tace taron ya nuna kyamarsa da kin amincewa wajan yin amfani da karfin Soja, wajan warware Matsalar Kasar Niger, maimakon haka a cigaga dayin amfani da hanyar Difilomasiyya kasancewar Nijeriyya da Niger duka abu daya ne.

Haka kuma taron yayi kira ga hukumomi su tashi tsaye wajan magance matsalolin shaye-shaye ga Matasa, rashin aikinyi da magance ayyukan assha da ake fama dasu daga bangaren Matasa.

Ba Zamu Bari Yunkurin Juyin Mulki yayi Nasara a Nigeria ba – Rundunar Soji

Taron yayi bayani akan irin yadda sufanci ya bada gudunmawa wajan yada ilimin addinin Musulunci tareda karantar da ingantacciyar fahimtar addinin Musulunci da yada zaman lafiya a tsakanin al’uma.

Kazalika taron ya bukaci Gwamnati a kowanne mataki su tallafawa al’umma domin rage radadin halin matsi da al’umar Kasar nan suke ciki.

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta Soke lasisin duk Makarantu Masu Zaman Kansu a jihar

Taron yaja hankalin iyaye akan su tsaya ga abunda ya zama wajibi akansu na tarbiyar ‘yayansu da kiyaye lafiyarsu, Mutuncinsu da karesu daga fadawa cikin miyagun ayyuka.

Haka kuma an bukaci al’umma su koma zuwa ga Allah da yin tuba da kamewa daga barin laifuka wadanda Allah ya hana, kyautata mu’amulla a tsakanin juna, tausayawa na kasa, domin yin hakan Allah zai dubemu da rahamarsa ya yaye mana halin da muke ciki.

Taron ya tsawatar wa masu fassara littattafan magabata da ra’ayin su ba tare da sanin abinda mawallafan suke nufi ba, domin kaucewa batanci ga marubutan da kuma dora Al’umma akan gurbatacciyar fahimta.

Taron kazalika yayi kira ga mabiya Darikar Tijjaniyya su cigaba da aiki da koyarwar Shehu Ahmadu Tijjani (RA) da Shehu Ibrahim Inyass (RA) suka dorasu akai.

Sanarwar ta ce taron daga karshe yayi addu’a ga shugabanni akan Allah yayi ruko da hannayensu yayi musu jagoranci kuma yasa tausayin Al’uma a zukatansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...