Rikicin Aure: Ya kamata Hukumar Hisba ta shiga tsakanin G-Fresh da Sadiya Haruna – Auwal Danlarabawa

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shugaban gidauniyar tallafawa mabukata tun daga tushe wato Grassroot Care anda Aid Foundation Amb. Auwal Muhammad Danlarabawa ya yi kira ga Hukumar Hisba ta jihar kano da ta gayyaci Sadiya Haruna da G Fresh Al’amin akan abubuwan da suke yi na wulakanta aure a sohiyal media dan kare martabar aure a Addini da al’ummar musulmi .

 

“Babu shakka idan hukumar Hisbah ta shiga wannan lamari za’a iya samun masalaha da daidaito a auren nasu kuma hakan zai kawo ƙarshen zubar da kimar Musulmi da Hausawa da ma’auratan biyu suke yi”.

Talla

Danlarabawa ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Kano.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta Soke Zaɓen Wani Dan Majalisar Tarayya a Kano

Ya Koka matuka kan irin kalamai na zubar da kima da ma’auratan suke yi a shafukansu na dandalin sada zumunta, wanda hakan bai dace ba, dukkuwa da cewa basu jima da yin aurenba.

” A koyarwar addinin musulunci da dabi’un Malam Bashaushe abubuwan da suke yi ba daidai ba ne, don haka nake kira ga Hukumar Hisba data gayyaci Sadiya Haruna da Mijinta G-Fresh Al-ameen don daidaita su ko kuma yin abun da ya dace game da auren nasu”. Inji Auwal Danlarabawa

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a kwanakin baya ne dai aka daura auren G-Fresh da Sadiya Haruna Kuma makonni kadan bayan auren sa’insa ta barke tsakanin su a shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...