Da dumi-dumi: ECOWAS ta bayyana matakin da zata dauka akan gwamnatin sojin Nijar

Date:

Daga Zainab Kabir Kundila

 

Shugabannin kungiyar ECOWAS sun ba da umarnin gaggauta daukar matakin amfani da karfin soji kan gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar. Sun kuma yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka, AU, da sauransu da su goyi bayan kudurin da kungiyar .

 

Kungiyar ECOWAS ta ce duk kokarin da aka yi na tattaunawa da gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, shugabannin juyin mulkin sun yi watsi da shi, yayin da suke yin Allah wadai da ci gaba da tsare shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa.

Talla

An cimma wannan matsaya ta shugabannin ECOWAS ne a taron koli na musamman kan harkokin siyasa a Jamhuriyar Nijar wanda ya samu halartar shugabannin kasashe takwas da ministocin harkokin wajen kasashen Laberiya da Gambia da aka kammala a Abuja.

Shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani da takwaransa na Burundi, Everiste Ndayishimiye sun halarci taron gaggawa na kungiyar ECOWAS karo na biyu kan Jamhuriyar Nijar bisa gayyatar abokan aikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...