Daga Rahama Umar Kwaru
A daren jiya Laraba ne Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sanusi ya ziyarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Sarki Sanusi ya isa fadar Villa ne da misalin karfe 8:25 na dare bayan wata babbar tawagar Malamai ta Najeriya data gana da shugaban kasar.
Tsohon Sarkin dai ya dawo ne daga Jamhuriyar Nijar inda ya gana da gwamnatin mulkin soja da ta kwace mulki daga hannun zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Kadaura24 ta ruwaito yadda Sanusi ya gana da shugabannin da suka yi juyin mulki Inda suja tattaunawa kan abun da ya shafi juyin mulkin.
Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily trust cewa Sanusi ya je Nijar din ne a radin kansa, amma gabanin tafiyarsa ya sanar da shugaba Tinubu .
Juyin Mulkin Nijar: Muhammad Bazoum ya bayyana halin da ya shiga a hannun sojojin Nijar
Tawagar da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS basu sami ganawa da shugabannin sojojin ba saboda sun ki yadda sa gana da su.
Amma a ranar Laraba, Hotunan Sanusi wanda shi ne shugaban Darikar Tijjaniya a Nigeria dake da dimbin magoya baya a Nijar, sun karade shafukan sada zumunta. shiga yadu.Sanusi shi ne Khal
Yayin ganawar Sanusi da Shugaban Mulkin Soji na Nijar yana tare da Sultan na Damagara,, wanda Damagaran shi ne birni na uku mafi girma a Nijar.
Majiyoyi sun shaida wa Daily trust cewa Sanusi ya je Nijar din ne domin ya bude kofa tattaunawa da gwamnatin mulkin soja. Daya daga cikin majiyar ta ce, “Mai martaba ya yi wannan tafiya ne a radin kansa, amma ba da sanin shugaban kasa Bola Tinubu ne biyo bayan damuwarsa game da rikicin da ake yi da kuma yadda za a shawo kan matsalar.
Taron ya zo kwana guda gabanin taron shugabannin ECOWAS a Abuja Tinubu, wanda shi ne Shugaban ECOWAS, ya shirya wani taro a ranar Alhamis bayan wa’adin kwanaki 7 da kungiyar ta fitar na maido da Bazoum mulkin kasar ya cika.