Daga Zainab Kabir Kundila
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf ta dauki aniyar chanjawa jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar kano KAROTA Kakinsu.
Shugaban Hukumar ta KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir, ne ya bayyana hakan a lokacin da jami’an hukumar na wucin gadi Marshal suka ziyarci a ofishinsa.

Yace za’a sauya musu kalar kayan da duk suke sanyawa a kokarin hukumar na Kara zaburar da ma’aikatanta don inganta aiyukan su a kano.
Da dumi-dumi: Ganduje ya baiwa tsohon kwamishinansa mukami
” Zamu yi duk mai yiyuwa wajen ganin mun Kara ingantawa da tsaftace aikin mu, Saboda jami’anmu su sami damar magance matsalolin da ake samu daga masu amfani da hanyoyi a fadin jihar kano”. Inji Engr. Faisal
Sai dai bai bayyana kalar da kakin na karotar zai koma ba, kamar yadda sanarwar da kakakin hukumar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar.
Idan za’a iya tunawa a baya dai an jima an ta rade-radin gwamnatin jihar kano zata sauya yan karotar kakaki saboda wasu dalilai masu nasa ba da Siyasa