Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Kamfanin Shirya Fina Finan Hausa na Maiwaya Film Production, Ya bayyana Shirin sa na fara daukar Sabon Film dinsa Mai Dogon Zango Mai Suna BOYAYAN MASOYI.
A cikin wani bayani da Shugaban kamfanin Sani Idris Maiwaya ya wallafa a Shafin sa na sada zumunta yace “Zamu yi amfani da Fasahar zamani wajen daukar wannan Sabon Film din ta yadda zaiyi goyayya da fitattun fina-finai masu dogon zango.

Ya Kuma cigaba da cewa akwai Sabbin kayan aiki na zamani da za’ayi amfani dasu don ganin an cimma nasarar da ake da bukata.
Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin Sanya hoton Muhd Sanusi II a dakin taro na Coronation
Haka Kuma akwai manyan jarumai da zasu taka rawa a cikin shirin dama Sabbin Jarumai duka a cikin Sabon film din mai Suna “BOYAYAN MASOYI”
Haka zalika ana sa ran Za a kwashe tsahon wata guda ana daukar. Aikin a Kano da jigawa da Kuma Katsina Wanda Ake sa ran fara daukar sa a cikin watan Agusta na 2023.
Da dumi-dumi: Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar Nigeria
Darakta Ibrahim Bala Shine Zai dauki Shirin Sai Mai taimaka masa Abdul Kangiwa
Yayin da Sani Idris Maiwaya ya Shirya Shirin
A karshe Shugaban kamfanin ya bukaci Al’uma dasu Taimaka da Addu’a Dan Samun Nasara.